27 Mayu 2015 - 09:56
Netanyahu; Iran ta fi IS hadari

Firaministan HK Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi ga kasashen Duniya cewa, barin Iran ta mallaki makamashin nukiliya na abu ne da ya fi kungiyar ISIL muni fiye da sau dubu. Netanyahu ya ce kungiyar ISIS barazana ce, amma ya danganta Iran a matsayin kasar ‘yan ta’adda.

Netanyahu ya ce matukar Iran ta mallaki makamashin  nukiliya za ta fi Kungiyar IS da ke da’awar Jihadi mugunta fiye da sau dubu.

Kalaman shugaban na Yahudawa na zuwa ne a yayin da kwararru daga bangaren Iran da manyan kasashen duniya ke shirin ganawa a Vienna kafin cikar wa’adin cim ma yarjejeniyar nukiliyar a ranar 30 ga watan Yuni.

Netanyahu ya dade yana adawa da sasantawar da kasashen Amurka da birtaniya da Faransa da Rasha da Jamus ke yi da Iran don cim ma yarjejeniya da ita akan yadda zata dakatar da shirinta na Nukiliya.

Idan ba a manta ba shirin makamashin Nukiliya na Iran na zaman lafiya.ABNA